IQNA

Sakon Fafaroma Francis dangane da fara azumin watan Ramadan

17:09 - March 11, 2024
Lambar Labari: 3490787
IQNA - A yayin da aka fara azumin watan Ramadan, shugaban mabiya darikar Katolika na duniya ya fitar da sakon hadin kai ga musulmi tare da bayyana cewa yana addu'ar Allah ya tabbatar da zaman lafiya a kasar Ukraine da kuma yankin gabas ta tsakiya.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na TRT cewa, Paparoma Francis shugaban mabiya darikar Katolika na duniya ya fitar da sakon nuna goyon baya ga musulmi dangane da fara azumin watan Ramadan.

Ya bayyana goyon bayansa ga al’ummar musulmi a kan azumin watan Ramadan a yayin bikin addu’ar a ranar Lahadi 20 ga watan Maris, wanda ya yi jawabi daga barandar ofishinsa ga dimbin jama’ar da suka halarci dandalin St.

Ya kara da cewa: A daren yau ne aka fara watan Ramadan na ‘yan uwa musulmi. Ina bayyana goyon bayana ga dukkansu.

Da yake nuni da cewa yana addu'ar samar da zaman lafiya a Ukraine da kuma yankin gabas ta tsakiya, shugaban mabiya darikar Katolika na duniya ya bayyana fatansa na ganin cewa za a kawo karshen tashe-tashen hankulan da ke janyo wa fararen hula wahala cikin gaggawa.

 

https://iqna.ir/fa/news/4204788

 

captcha