IQNA

Shahadar wasu matasan Falasdinawa biyu a yammacin gabar kogin Jordan

16:56 - September 01, 2022
Lambar Labari: 3487782
Tehran (IQNA) Wasu matasan Palasdinawa biyu sun yi shahada a garuruwan Al-Bira da Nabul bayan da sojojin yahudawan sahyuniya suka harbe su.

A cewar cibiyar yada labaran Falasdinu, a safiyar Alhamis din nan ne sojojin mamaya na Isra'ila suka bindige wasu matasan Palasdinawa biyu a lokacin da suke kai hare-hare masu yawa da aka kai a yankuna daban-daban a yammacin gabar kogin Jordan.

Majiyar likitocin Falasdinu ta sanar da cewa, an harbe Yazen Afaneh, mazaunin sansanin 'yan gudun hijira na Qalandiya, a yayin harin da sojojin mamaya suka kai a unguwar Umm al-Sharayt a garin Al-Bira, wanda aka yi tashe tashen hankula.

Har ila yau, "Samer Khaled" mazaunin sansanin Al-Ain, ya mutu sakamakon munanan raunuka da ya samu a yayin harin da sojojin mamaya suka kai a sansanin 'yan gudun hijira na Balata da ke gabashin Nablus.

Bayan gagarumin farmakin da dakarun yahudawan sahyuniya suka kai sansanin 'yan gudun hijira na Balata, an yi ta samun kazamin fada tsakanin su da 'yan adawa.

 

4082414

 

 

captcha