IQNA

Yarinya 'Yar Shekaru 14 Ta Zo Ta Daya A Gasar Kur'ani Ta Azhar

22:56 - October 01, 2021
Lambar Labari: 3486372
Tehran (IQNA) Fatima Atef Albandari 'yar shekaru 14 da haihuwa ta zo ta daya a gasar kur'ani ta cibiyar Azhar.

Shafin yada labarai na Akhbarul yaum ya bayar da rahoton cewa, an fitar da sakamakon gasar kur'ani ta cibiyar Azhar wadda dubban dalibai suka shiga, inda Fatima Atef Albandari 'yar shekaru 14 da haihuwa ta zo ta daya a wannan gasa.

Fatima albandari dai an haife ta ne a garin Alkharija da ke cikin gundumar wadil jadid a kasar Masar a shekara ta 2007.

Ta samu tarbiyar addini daga wajen mahaifanta tun tana karama, kuma ta fara karatun kur'ania  gaban mahaifinta kafin zuwa makaranta.

mahaifin Fatima ya bayyana cewa, diyarsa ta hardace dukkanin kur'ani mai tsarki tana da shekaru tara da haihuwa.

A halin yanzu tana aji na uku ne makarantar sakandare, inda ko a bangaren karatun boko, tana daga cikin dalibai masu matukar hazaka.

4001251

captcha