IQNA

Babban Shehin Azhar: Idin Layya Babbar Dama Ce Ta Hadin Kai Tsakanin Dukkanin Musulmi

20:19 - July 19, 2021
Lambar Labari: 3486118
Tehran (IQNA) babban malamin cibiyar ilimi ta Azhar ya bayyana lokacin idin layya da cewa babbar dama ce ta hadin kai tsaknin musulmi.

Shafin jaridar Al-ittihad ya bayar da rahoton cewa, a cikin wani bayani da ya fitar a yau litinin, Sheikh Ahmad Tayyib babban malamin cibiyar ilimi ta Azhar ya bayyana lokacin idin layya da cewa babbar dama ce ta samun hadin kai tsaknin al'ummar musulmi.

Haka nan kuma Shehin malamin ya bayyana cewa, lokacin idin layya lokaci ne mai albarka, wanda ake gudanar da ayyuka na ibadar hajji, da sauran ayyuka da suka kebanci wannan lokaci mai albarka, wanda ya ce shi ma hakan yana a matsayin dama ga musulmi da su yawaita ayyukan alkhairi a cikinsa, da hakan ya hada da taimakon marassa karfi, da marassa lafiya, da kyautawa makusanta.

Shehin malamin kuma ya yi ishara da irin matsalolin da duniyar musulmi ta samu kanta a ciki a bangarori daban-daban, wanda ya ce samun mafita dangane da hakan na bukatar komawa ga Allah, da kuma ajiye sabanin fahimta a gefe guda tsakanin musulmi, dom,in yin aiki tare wajen fuskantar kalubalen da ke a gaban duniyar musulmi a  yau.

Daga karshe ya yi fatan samun zaman lafiya da kwanciyar hankali da wadatar arziki a dukkanin kasashen musulmi na duniya.

 

 

 

3985036

 

 

captcha