IQNA

Cibiyar Musulmin Kasar Canada Tana Bayar Da Tallafi Ga Marassa Galihu A Kasar

22:22 - December 23, 2020
Lambar Labari: 3485486
Tehran (IQNA) cibiyar musulmin yankin Yellowknife a kasar Canada tana bayar da tallafi ga marassa galihu a kasar.

Shafin yada labarai na jaridar The Star ya bayar da rahoton cewa, cibiyar musulmin ta Canada ta bayar da daurin kwalaye dake dauke da tallafin kayan bukatar rayuwa, musamman a lokacin corona da kuma yanayin hunturu.

Rahoton ya ce ciyar ta bayar da wani bangare na taimakon ga cibiyar ayyukan jin kai ta YWCA ta Canada domin raba wag a jama’a mabukata.

Nazem Awwan shi ne bababn daraktan cibiyar ta Yellowknife, ya kuma bayyana cewa taimakon nasu ya hada musulmi da wadanda ba musulmi ba, domin su burinsu shi ne su taimaka ma mutane mabukata kamar yadda addinin musulunci ya yi umarni.

Koa  shekarar da ta gabata cibiyar musulmin yankin na Yellowknife ta bayar da tallafi irin wannan ga mabukata a kasar Canada.

3942905

 

 

 

captcha