IQNA

An Yi Janazar Yaron Da Sojojin Yahudawan Isra'ila Suka Harbe Shi Da Bindiga A Falastinu

23:21 - December 06, 2020
Lambar Labari: 3485435
Tehran (IQNA) an gudanar da janazar matashi bafalastine da sojojin yahudawan Isra'ila suka kashe a Bait Lahm.

A jiya Asabar ne aka yi jana’izar matashin Bafalasdinan nan dan shekara 13 da ya yi shahada sakamakon harbin bindiga na sojojin yahudawan mamaya na Isra’ila a gaɓar yammacin Kogin Jordan.

Daruruwan Falasdinawa suka halarci jana’izar tasa duk da halin da ake ciki na annobar korona.

A ranar Juma’a data gabata ce sojojin Isra’ilar suka harbe matashin mai suna Ali Ayman Abou Aliya, wanda ya yi shahada a gadon asibiti, inda yake jinya sakamakon shiga jikinsa da harsashi ya yi.

Kafin hakan dai dubban Falasdinawa ne ke gudanar da zanga-zanga a Gaza, domin nuna rashin amincewa da shirin Isra'ila na mamaye yankin gabar yamma da Kogin Jordan.

Masu boren na daga tutocin Falasdinawa, suna kuma yin Allah wadai da Shugaba Trump na Amurka kan goyon bayan da ya nuna ga shirin Isra'ilar.

3939237

 

captcha