IQNA

Ayatollah Isa Qasem Ya Isar Da Sakon Ta’aziyyar Rasuwar Ayatollah Taskhiri

23:04 - August 18, 2020
Lambar Labari: 3485099
Tehran (IQNA) babban malamin addini na kasar Bahrain Ayatollah Isa Qasem ya isar da sakon ta’aziyyar rasuwar Ayatollah Taskhiri.

Ayatollah Isa Qasem babban malamin addini na kasar Bahrain ya isar da sakon ta’aziyyar rasuwar Ayatollah Taskhiri wanda Allah ya yi masa rasuwa a yau bayan fama da rashin lafiya.

A cikin sakon ya bayyana cewa:

Ga Allah muke kuma zuwa gare shi ne za mu koma

A cikin alhini ina mai isar da sakon ta’aziyyar rashin babban malamin addinin musulunci Ayatollah Muhammad Taskhiri, wanda rashinsa babban rashi ne ga dukkanin malamai da mujahidai da masu son adalci da hadin kai tsakanin al’ummar musulmi.

Ya ce hakika an yi rashin babban mutum ta fuskar ilimi, hankali, imani, gaskiya, sadaukarwa, kyawawan dabi’u, son gaskiya da adalci da taimakon raunana a duniya, da kuma hada kan al’ummar musulmi.

Muna rokon Allah madaukakin sarki da ya jikansa da rahma ya gafarta masa, ya kuma bai wa iyalansa hakurin rashinsa.

 

3917459

 

captcha