Tashar Russia Today ta bayar da rahoton cewa, Tedros Adhanom babban daraktan hukumar lafiya ta duniya WHO ya bayyana cewa, yin amfani da kalmomi da ke nuni da cewa cutar corona ta mamaye duniya, suna saka tsoro da firgici a cikin zukatan mutane a duniya.
Ya kara da cewa, yin amfani da irin wadannan kalmomi za su sanya ayi zaton cewa hukumomin lafiya na kasashen sun gaza wajen tunkarar wanann cuta, wanda kuma ba haka ba ne, domin kuwa suna yin iyakacin kokarinsu.
Haka nan kuma babban daraktan na hukumar lafiya ta duniya ya nuna damuwa kan yaduwar cutar a kasashen Koiya ta kudu da Italiya da kuma Iran.