IQNA

Kur’ani Na Karni Na 17 A Birnin Beirut

22:20 - July 16, 2017
Lambar Labari: 3481705
Bangaren kasa da kasa, an nuna wani kwafin kur’ani mai tsarki a wani baje koli a birnin Beirut inda aka nuna wani kur’ani da tarihinsa ke komawa zuwa ga shekarar 1740.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin middle east online cewa, Eami Nimr wani bapalastine da aka haifa abeirut ta kasar Lebanon ya gudanar da wani bae kolin dadaddun kwafin kur’anai.

Wannan dai bas hi karon farko da yake yin hakan ba, domin nkuwa daya daga ciin muhimman ayyukan da ya sanya a gaba shi ne, tattara kwafin kur’ani musamman dadaddudomin adana su da kuma gano tarihinsu da lokacin rubuta su.

A wanann karon ma ya nuna wannan kur’ani wanda asalinsa daga nahiyar Afirka ne, kuma an rubuta shi da hannu tuna cikion karni na 1740 miladiyya, inda yake ci gaba da adana shi.

Mutane da dama ne suke halartar wannan baje koli na dadaddun kur’anai da wannan mutum yake gudanarwa tare da hadin gwaiwa da bangarorin kla da adana kayan tarihi na kasar.

Wannan dan kasuwa bapalastine ya bayyana cewa, an kai wanann kur’ani zuwa kasar Amurka ne,a lokacin da trawa suke kwasar mutane daga nahiyar Afirka zuwa kasashensu domin bautar da su.

A cikin shekaru 1500 zuwa 1800 ne cinikin bayi ya yi yawa tsakanin kasashen turai daga nbahiyar Afirka, wanda hakan ya sanya aka samu bakaken fata da dama a cikin kasar Amurka da ma Birtaniya.

3619177

captcha