IQNA

Maniyyata Dubu 6 Ne Daga Kasar Kenya Za Su Sauke Farali A Bana

23:17 - April 03, 2017
Lambar Labari: 3481372
Bangaren kasa da kasa, maniyyata dubu 6 za su sauke farali a bana daga kasar Kenya bayan kara yawan adadin alhazan kasar.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, hukumar kula da ayyukan hajji da Umra ta kasar saudiyya ta kara yawan mahajjatan Kenya daga dubu hudu zuwa dubu shida a kowace shekara.

Bayanin ya ci gaba da cewa, wannan shi ne karo na farko da wannan adadi na musulmin kasar Kenya za su halarci taron aikin hajji domin sauke farali.

Sharif Hussain Umar shi ne mataimakin shugaban hukumar kula da ayyukan hajji da Umra ta kasar Kenya, ya bayyana cewa tuni suka fara gudanar da dukkanin abubuwan da suka gabata domin ganin maniyyata sun kammala shirinsu, da hakan ya hada da karbar fasfo domin shirya batun visa.

Ma’aikatar kula da harkokin aikin hajji ta Saudiyyah ta sanar da cewa, za ta bayar da visa ga alhazan kasar Kenya ta hanyar yanar gizo ne kai tsai tsaye.

3586492

captcha