Sayyid Nasrullah ya bayyana cewa kisan gillar da masarautar ‘ya’yan Saud ta yi a kan fararen hula a ranar asabar da ta gabata a birnin San’a na kasar Yemen aiki ne na dabbanci da rashin imani.
Ya ce hakika abin kunya ne ga masu ikirarin cewa suna kare martabar haramomi masu tsarki guda biy su aikata danyen aiki na kisan gilla a kan fararen hula musulmi a cikin wannan wata wanda aka haramta zubar da jinni a cikinsa.
Sayyid Nasrullah ya ce a wannan shekara tarukan ashura a ranar goma ga watan muharram za su hada da juyayin ashura da kuma kisan kiyashin da aka yi wa musulmi a Yemen a hannun mashaya jini masu kwadayin zubar da jini na bayin Allah.
Wanann mataki shi ne irinsa da kungiyar Hizbullah ta dauka a lokacin da yahudawan sahyuniya suke ruwan bama-bamai a kan al’ummar yankin zirin Gaza, inda aka gudanar da Ashura tare da yin juyayi da alhini kan kisan kiyashin da Isra’ila take kan al’ummar Gaza a lokacin, wanda kuma a wannan karon masarautar Saudiyya ce take tafka irin wannan aiki na Isra’ila amma a kan al’ummar Musulmi na Yemen.
Sayyid Nasrullah ya ce yan akira ga wadanda za su fita aranar Ashura da su daga tutocin Imam Hussain (AS) a lokaci guda kuma su daga totocin kasar Yemen, domin nuna goyon bayansu ga musulmin Yemen da Saudiyya ke ma kisan kiyashi.