IQNA

Wasu Daga Malaman Yankin Al-awamiyyah Sun Bukaci Yin Afuwa Ga Ayatollah Nimr

22:28 - November 06, 2015
Lambar Labari: 3443993
Bangaren kasa da kasa, wasu daga cikin malaman mabiya tafarkin shi’a a yankin Al-awamiyyah sun bukaci da a yi wa Ataollah Nimr afuwa kan hukuncin da aka yanke masa.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na «qatifnews.com»  cewa, wasu daga cikin malaman shi’a a yani Al-awamiyyah a gabacin Saudiyyah, sun bukaci sarki Salman na Saudiyya da ya yi afuwa Aytaollah Nimr da sauran wadanda aka yanke ma hukuncin kisa da ake tsare da su.

Daga cikin malaman akwai Sheikh Nazir Zahir, Sheikh Ali Al Zaid, Shiek Farid Shuyukh, Sayyid Yusuf Abbas, Sayyid Mahdi Sadat, Sayyid Said Al Jamal, da Sheikh Naji Al-imadi, duk sun sanya hannu kan takardar.

Rahotanni sun cewa al’ummar Saudiyya da suke gabashin kasar suna ci gaba da gudanar da zanga-zangar nuna goyon bayansu ga Sheikh Nimr Baqir Nimr da mahukuntan kasar suka yanke masa hukuncin kisa.

Tun daga daren Alhamis yau dare uku a jere ke nan al’ummar garin da ke gabashin Saudiyya suke gudanar da zanga-zangar jaddada goyon bayansu ga sheikh Nimr Baqir Nimr malamin ‘yan shi’a da ke gwagwarmayar neman ‘yanci daga bakar siyasar zalunci da babakeren gidan Saurautar kasar.



Masu zanga-zangar suna rera taken yin gargadi ga mahukuntan kasar ta Saudiyya kan nisantar zartar da hukuncin kisa kan Sheikh Nimr Baqir Nimr tare da hanzarta sakinsa.



Tun dai wata kotu a kasar ta Saudiyya ta yanke hukuncin kisa kan sheikhin malamin saboda shahararsa a fagen yaki da nuna bambanci a tsakanin ‘yan kasar tare da neman aiwatar da tsarin dimokaradiyya da zai kawo karshen babakere mahukuntan kasar.



3443903

Abubuwan Da Ya Shafa: saudiyyah
captcha