IQNA

‘Yan ta’addan daesh Sun Dauki Alhakin Kai Hari Kan husainiyar ‘Yan shia A Saudiyyah

23:09 - October 17, 2015
Lambar Labari: 3386754
Bangaren kasa da kasa, kungiyar yan ta’adan Daesh reshen Wilayat Bahrain ta dauji alhakin kaddamar da harin ta’addanci a akn mabiya iyalan gidan manzon Allah a Saudiyya.


Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Sky News Arabic cewa, yan ta’adan Daesh reshen Wilayat Bahrain ta dauki alhakin kaddamar da harin ta’addanci a akan mabiya iyalan gidan manzon Allah a a Husainiyar Haidariyyah a yankin Qatif dake gabacin kasar Saudiyya

A kalla mutane biyar ne masu zaman juyayin Ashura’ su ka yi shahada a Saudiyya sanadiyyar harin ta’addanci da aka kai musu a jiya da dare.

Kamfanin Dillancin Labarun Faransa ya ambato ma’aikatar harkokin cikin gidan Saudiyyar tana cewa; Mutane biya rne su ka kwanta dama bayan bude wuta da aka yi a kusa da masallacin da ke garin Saihat da ke gundumar Qatif a gabacin Saudiyya.

Kakakin ma’aikatar harkokin Wajen Saudiyyar ya ce; Da misalin karfe bakwai na marecen jiya juma’a ne jami’an tsaro su ka tsinkayi wani mutum wanda ya ke dauke da makami a kusa da wani masallaci da ke unguwar Kauthar a garin Saihat na gudumar Qatif, inda ya bude akan mutanen da ke wucewa a masalacin.”

Jami’in ma’aikatar harkokin wajen na Saudiyya ya ci gaba da cewa; Jami’an tsaro da su ke sintiri a wurin sun bude wuta akan mutumin tare da kashe shi nan take.”

Kawo ya zuwa dai an tabbatar da mutuwar mutane biyar da  su ka hada da mace da kuma jikkatar wasu mutane tara.

A shekarar da ta gabata ma dai wasu ‘yan ta’addar sun kashe mutane 7 a wata Husainiyyah da ta ke garin Dalwah a gundumar Ahsa’a a gabcin Saudiyyar.

Kungiyar ‘yan ta’adda ta Da’esh,  Isil reshen Kasar Bahrain ta sanar da daukar kai harin na jiya a Saudiyya.

3386119

Abubuwan Da Ya Shafa: saudiyyah
captcha