IQNA

Janazar Wadanda Suka Yi Shahada A Harin Masallacin Imam Hussain (AS) A Dammam Saudiyyah

23:42 - June 04, 2015
Lambar Labari: 3310922
Bangaren ksa da kasa, an gudanar da janazar mutaen da suka yi shahada a harin ta'addancin da aka kai a masallacin Imam Hussain (AS) a garin Dammm a yankin Al-anud dake birnin.


Kamfanin dillancin labara Iqna ya habrat cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Al-alam cewa, a jiya an gudanar da janazar mutaen da suka yi shahada a harin ta'addancin da aka kai a masallacin Imam Hussain (AS) a garin Dammam na yankin Saihat a kasar Saudiyyah, tare da halartar malamai na addin.

Masu janazar sun ta rera taken cewa mahukuntan kasar ta Saudiyya ne ke da alhakin daure ma wadanda ke gudanar da ayyukan ta'addanci gindi, kuma su ne kara yada koyarwa da ke kawo Baraka tsakanin al'ummar musulmi na kasar da sunan banbamcin fahimta ta addini.

Mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah mazauna yankin Dammam da sauran yankunan gabacin kasar ta Saudiyya sun jima suna fuskantar matsin lamba daga mahukuntan kasar, kafin daga baya a fara tura musu yan ta'adda suna kashe, kamar yadda aka gania  cikin wannan makoa masallacin Imam Hussain (AS) inda wani dan ta'adda ya tarwatsa kansa.

Wannan dan ta'adda ya yi kokarin shiga bangaren mata ne a cikin masallacin bayan da ya saka kayan mata, amma masu kula da masallacin sun hana shi shiga bayan da suka gane cewa namiji ne, saboda haka ya tarwatsa kansa a cikin garejin masallacin.

Tarwatsewar bam din dai ta yi sanadiyyar yin shahadar wasu daga cikin masu kula da tsaron masallacin, wadanda suka sadaukantar da rayuwarsu domin kare sauran mumunai da ke gudanar da salla da ayyukan ibada a cikin wanann masallaci, daga cikin waada suka yi shahada kuwa har da Abduljalil Al-arbash, Muhammad Isa.

3310870

Abubuwan Da Ya Shafa: saudiyyah
captcha