IQNA

Mahukuntan Saudiyya Na Son Tsorata 'Yan dawa Da Kuma Jawo Masu Tsatsauran Ra'ayi

22:54 - November 11, 2014
Lambar Labari: 1472350
Bangaren kasa da kasa, bababn limamamin masalalcin Imam Rida (AS) da ke birnin Sydney na kasar Australia Sheikh Farhat Amuli ya bayyana cewa gwamnatin saudiyya tana son ta shafe masu adawa da ita ne baki daya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a zantawarsa da limamamin masalalcin Imam Rida (AS) da ke birnin Sydney na kasar Australia Sheikh Farhat Amuli ya bayyana cewa gwamnatin saudiyya tana son ta shafe masu adawa da ita ne baki daya tare da jawo masu tsatsauran ra'ayi kafirta musulmi zuwa kusa da ita..

Mahukuntan Saudiyya sun yanke hukuncin kisa kan Sheikh Al-Nimir Nimir daya daga cikin manyan malaman addinin Musulunci mabiya mazhabar Shi’a a kasar Saudiyya.
Kamfanin dillancin labaran ya watsa rahoton cewa; Wata kotun da ke shari’ar manyan laifuka a birnin Riyidh na kasar Saudiyya a yau Laraba ta fitar da hukuncin kisa kan Sheikh Al-Nimir Nimir malamin addinin Musulunci kuma mai rajin kare hakkokin al’ummar da ake zalunta mabiyin mazhabar iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka {a.s} dan kasar ta Saudiyya kan zargin kunna wutar fitina tare da bijirewa shugaban Musulmi wato sarkin kasar.
Sheikh Al-Nimir Nimir dai ya yi fice a fagen kare hakkokin al’ummar Saudiyya musamman ‘yan tsirarun kasar mabiya mazhabar shi’a tare da nuna kin amincewa da bakar siyasar zaluncin mahukuntan Saudiyya gami da nuna goyon baya ga al’ummun da ake zalunta a duniya musamman al’ummar kasar Bahrain da ke makobtaka da Saudiyya.
Kungiyoyin kare hakkin bil adama da dama a kasashen duniya sun fara jan kunnen mahukuntan kasar Saudiyya dangane da hukuncin da wata kotun kasar ta yanke a kan daya daga cikin manyan malaman mazhabar shi'a a kasar, Sheikh Namir Muhammad Baqir Namir. 
Kotun kasar ta Saudiyya dai ta yanke hukuncin kisa ne a jiya Laraba a kan Sheikh Namir, bisa tuhumarsa da sukar salon mulkin mulukiya na masarautar Al-saud a kasar ta Saudiyya a cikin hudubobin sallar Juma'a da yake gabatarwa a masallacinsa da ke yankin Awamiyya a cikin gundumar Qatif da ke gabacin kasar.
Gamayyar wasu kungiyoyin kare hakkin bil adama a kasar Birtaniya da ma wasu kasashen turai da na larabawa, sun gargadi mahukuntan kasar ta Saudiyya da su shiga taitayinsu a kan hankoronsu na ganin sun kashe Sheikh Namir, wanda a cewar kungiyoyin aiwatar da wannan hukunci na siyasa zai jefa kasar cikin wani mawuyacin hali, wanda masarautar kasar ce za ta dauki alhakin hakan.
Sheikh Namir dan shekaru hamsin da biyar da haihuwa ya sahara a kasar Saudiyya da ma kasashen larabawa, wajen gwagwarmayarsa ta kare hakkokin mutane da ake zalunta, da kuma bude cibiyoyin ilimi da wayar da kan al'umma kan harkoki na zamantakewa da kuma siyasa a addinance, wannan ya sanya shi ya samu karbuwa a wajen mutane da dama a kasar ta Saudiyya, mabiya mazhabar shi'a da ma wadanda ba su ba, musamman talakawa daga cikin mutanen kasar, sakamakon tunkarar sarakunan kasar da yake yi tare da fada musu gaskiya, abin da sauran malaman kasar ba za su iya yi ba.

A cikin watan Agustan dubu biyu da takwas gwamnatin Saudiyya ta kafa masa takunkumin na hana shi gabatar da laccoci ko fitar da makaloli da sauran rubuce-rubuce da ya saba yi, na addini ne ko na siyasa ko kuma na zamantakewa, tare da sanya idon  jami'an tsaro a kansa.
A cikin watan Oktoban shekara ta 2011 al'ummomi a yankunan Qatif da Ihsa da kuma Awamiyyah da ma sauran yankunan gabacin Saudiyya wanda akasarin mazauna wadannan yankuna mabiya mazhabar shi'a ne, kuma a nan ne dukkanin arzikin danyen manfetur da iskar gas da kasar Saudiyya take da shi yake, suka fito suna nuna rashin amincewarsu da salon mulkin mulukiya na kasar, tare da neman a saki dubban fursunonin siyasa da mahukuntan kasar suke tsare da su, tare da neman a yi adalci wajen rabon arzikin kasar musamamn ma ganin cewa arzikin manfetur da iskar gas da kasar Saudiyya ta dogara da shi daga yankinsu ake fitar da shi, amma mahukuntan kasar sun yi amfani da karfi wajen murkushe su tare da kashe adadi mai yawa da kuma kame wasu dubbai daga cikinsu, wanda hakan ya sanya Sheikh Namir ya fito ya soki wannan mataki da mahukuntan kasar suke dauka kan fararen hula masu zanga-zangar lumana domin neman hakkokinsu da aka haramta musu.

1471841

Abubuwan Da Ya Shafa: saudiyyah
captcha