IQNA

Kur'ani mai girma; A cikin jerin littattafan da aka fi siyarwa a duniya

16:51 - April 24, 2024
Lambar Labari: 3491036
IQNA - Cibiyoyin bincike masu alaka da sa ido kan al'amuran al'adu sun bayyana kur'ani mai tsarki a matsayin daya daga cikin litattafan da aka fi sayar da su a duniya.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-Akhbar al-Masa’i cewa, a ranar 23 ga watan Afrilun da ya gabata (4 ga watan Mayu) ta yi daidai da ranar littafai ta duniya da hukumar UNESCO ke gudanar da ita a duk shekara.

A ranar littafai ta duniya, UNESCO, tare da hadin gwiwar sauran kungiyoyin kasa da kasa masu alaka da littattafai, sun zabi birni a matsayin babban birnin litattafai na duniya.

 Makasudin zabar irin wannan birni shi ne don a kwadaitar da jama’a gaba daya da kuma matasa musamman wajen gano farin cikin karatu da mutunta ayyuka da ilimin da marubuta suka kirkira tsawon shekaru aru-aru. Bugu da kari, domin yada al'adu a tsakanin jama'a, babban littafin da aka zaba ya kan yi duk shekara don inganta karatu da kuma kara yawan karatu a kungiyoyi daban-daban na shekaru daban-daban da kuma al'umma a ciki da wajen kasar. 

A ranar littafai ta duniya ta bana, Darakta-Janar na UNESCO, Audrey Ozolai, ya ba birnin Accra na kasar Ghana taken babban birnin littafai na duniya a shekarar 2024.

Duk da ci gaban da ake samu na fasaha da kuma yadda mutane ke samun damar shiga Intanet da shafukan sada zumunta, har yanzu littattafai sun shahara sosai a duniya. Kowace shekara mawallafa a duniya suna buga dubban littattafai kuma wasu daga cikinsu suna gasa da juna don samun mafi kyawun masu sayarwa.

Cibiyoyin bincike a duniya sun sanar da cewa kur’ani mai tsarki, Nahj al-Balagha, Usul Kafi da Asfar Arbaa na daga cikin litattafan da aka fi sayar da su a duniya, musamman a kasashen musulmi.

4212109

 

 

 

captcha