IQNA

Masaallatan Canada sun Taimakawa wadanda ibtila’I ya shafa a Libiya da Maroko

16:00 - September 17, 2023
Lambar Labari: 3489829
Masallatai da cibiyoyin addinin musulunci da dama a kasar Canada sun tattara tare da aike da kayan agaji domin taimakawa wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a Libiya da Maroko.
Masaallatan Canada sun Taimakawa wadanda ibtila’I ya shafa a Libiya da Maroko

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na CBC cewa, a yayin da al’ummar kasar Libya mazauna kasar Canada ke cikin alhinin bala’in ambaliyar ruwa da aka yi a kasar, masallatai na kasar Canada na ci gaba da tattara kayan agaji ga wadanda abin ya shafa.

Masallatai a Kitchener da Waterloo suna tattara tallafi don aika wa wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a Libiya da girgizar kasa a Maroko.

Mambobin al'ummar kasar Libiya da ke zaune a yankin Waterloo da Guelph sun ce babu wata magana da za ta bayyana irin barnar da ambaliyar ruwa ta haddasa a gabashin Libiya. An ce adadin wadanda wannan ambaliya ya rutsa da su na iya kaiwa mutane dubu 20.

Abdulmanan Seyed limamin masallacin Waterloo ya ce: Mun san abin da za mu yi kadan ne, amma za mu yi kokarin yin namu.

Ya kara da cewa: "Bukatar tana da yawa, don haka muna yin iya kokarinmu don karfafa gwiwar mutane su taimaka musu gwargwadon iko."

Kungiyar matan Afirka ta yankin Waterloo (AWAWR) ta ce kungiyar tana goyon bayan al'ummar Libiya da Moroko a wannan mawuyacin lokaci. Kungiyar ta bayyana a shafin Facebook cewa mambobinta suna tunanin 'yan kasar Libya a yankin Waterloo, musamman wadanda wannan bala'i da ba a iya misaltawa ya shafa ya shafi 'yan uwansu.

Afzaleh Balogun, Babban Darakta na AWAWR ya ce: Kungiyarmu kungiya ce ta dukkan al'ummomin Afirka; Muna magana ne game da rayukan da aka yi asarar.

Ya kara da cewa: Ambaliyar ruwa a Libya da girgizar kasa a Maroko sun sanya kungiyar ta yi tunanin taimaka wa iyalan wadanda lamarin ya shafa. "Mun yi magana game da yadda za mu iya inganta a matsayinmu na mutane tare da juna da kuma a cikin al'ummominmu," in ji shi.

Sashen Sabis na Al'ummar Musulmi na yankin Waterloo kuma yana ba da sabis na shawarwari kyauta ga al'ummar Libya da na Moroccan na gida.

 

 

 

 

https://iqna.ir/fa/news/4169346/

Abubuwan Da Ya Shafa: libya girgizar kasa mai tsanani mutane
captcha