IQNA

Iran Ta Yi Allawadai Da Ci Gaba Da Yin Batunci Ga Manzon Allah (SAW) A Faransa

0:05 - October 25, 2020
Lambar Labari: 3485302
Tehran (IQNA) Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa, ci gaba da yin batunci da tozarci ga manzon Allah (SAW) a kasar Faransa abin Allawadai ne.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Saeed Khatib Zadeh ya ce, babu wata hujja ko dalili da za a iya kare abin da yake faruwa na cin zarafin addinin musulunci da keta alfarmar abubuwa masu tsarki na addini da ake yi a kasar Faransa.

Ya ci gaba da cewa, keta alrfamar manzon Allah (SAW) da ci zarafinsa, yana a matsayin keta alfarma da cin zarafin musulmi sama da biliyan 1 da miliyan 800 ne da ke duniya, wanda babu wani hankali da zai amince da haka da sunan ‘yancin bayyana albarkacin baki.

Haka nan kuma ya yi ishara da wasu matakai makamantan haka da wasu suka dauka a cikin wasu kasashen turai, da hakan ya hada da keta alframar kur’ani mai tsarki, inda gwamnatocin wadannan kasashen suke bayyana hakan a matsayin lamari da dokar kasashensu ta halasta yi.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Iran ya ce, ko alama musulmi ba su goyon bayan duk wani aiki na ta’addanci da sunan musulunci, kamar yadda kuma ba su goyon bayan duk wani aiki na ta’addanci da nuna kyama a gare su saboda addininsu.

 

3930986

 

captcha