IQNA

Mayakan Haftar Na Ci gaba Da Kara Kutsawa A Cikin Birnin Tripoli

23:58 - April 30, 2019
1
Lambar Labari: 3483592
Kakakin rundunar Halifa Hatar da ke kaddamar da hare-hare kan birnin Tripoli na kasar Libya, suna ci gaba da kara kutsa kai a cikin birnin.

Kamfanin dillancin labaran iqna, tashar Russia Today ta bayar da rahoton cewa, kakakin rundunar Haftar Ahmad Al-mismari ya fadi jiya cewa, mayakansu na ci gaba da kara nausawa a cikin birnin, kuma suna kwace muhimman wurare, da hakan ya hada da yankin Salahuddin da ke birnin.

Ya kara da cewa, kwace muhimamn wurare zai taimaka musu wajen kammala kwace birnin cikin kankanin lokaci a nan gaba.

Shedun gani da ido sun ce ana matsanancin gumurzu tsakanin dakarun gwamnatin Libya, da kuma dakarun Haftar a yunkurin da suke yi an kwace iko da barin sojoji dake yankin Yarmuk a gefen birnin Tripoli, da kuma babban kwalejin ‘yan sanda , da kuma ofishin hukumar kula da shige ta fice ta kasar.

Aftar dai yana samun dauki ne da taimako daga kasashen Saudiyya, UAE da kuma Faransa, kamar yadda shugaban Amurka Donald Trump yana daga cikin masu mara masa baya.

 

3807470

 

 

 

 

 

Wanda Aka Watsa: 1
Ana Cikin Dubawa: 0
Ba A Iya Watsa Shi: 0
Ba A San Shi Ba
0
0
Asm ni ra ayina shine duniyar musulmi fa su sani muhammad bin salman fa ba addini yake kare wa ba ya bad da sahu ne don yayaki musul mai (haza wasalam)
captcha