IQNA

A Yau Ne Ake Rufe Gasar Kur’ani Ta Dubai

22:30 - June 03, 2018
Lambar Labari: 3482722
Bangaren kasa da kasa, a yau ne ake rue gasar kur’ani ta duniya a birnin Dubai na kasar hadaddiyar daular larabawa.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a yau ne ake rue gasar kur’ani ta duniya a birnin Dubai na kasar hadaddiyar daular larabawa tare da halartar manyan baki da suka hada da Sheikh Ali Abdurahman Alhuzaifi limamin masallacin manzo.

Ibrahim Bumalha shugaban kwamitin shirya gasar ya bayyana cewa, Huzaifi za iso da yammacin yau, kamar yadda uma wasu baki daga wasu kasashen duk za sui so, yayin da kuma wasu tuni sun rga sun iso.

Sa’id Harib mataimakin shugaban kwamitin gasar ya bayyana cewa, gasar ta gudana cikin nasara, kuma a daren yau ne za a bayar da kyautuka ga wadanda suka nuna kwazo, gasar ta samu halartar wakilai daga kasashe 104.

A ranar karshe wakilai daga kasashen Nigeria, Mauritaniya, Komoros, Chechniya, Masar, Azarbaijan, Togo, da Rasha ne suka kara da juna.

Wannan dai shi ne karo na ashirin da biyu da ake gudanar da wannan gasa da duniya a birnin Dubai.

3720024

 

 

 

 

captcha