IQNA

Taron Bayar Da Horo Kan Ayyukan Banki A Mahangar Musulunci A Sudan

21:22 - December 07, 2016
Lambar Labari: 3481012
Bangaren kasa da kasa, ana gudanar da wani zaman bayar da hook an harokin banki a mahangar sharia a birnin Khartum na kasar Sudan.


Kamfanin dilalncin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran kasar Saudiyyah cewa, an fara gudanar da wannan taron ne da nufin koyar da jami’an harkokin bankunan kasashen musulmi yadda ake yin mu’amala ta banki a mahagar shari’a.

Rahoton ya ce kwararru daga kasashen UAE, Bahrain, Kuwait, Turkiya da kuma Nigeria, suna halartar wannan taron.

Daga cikin abubuwan da ake bayar da horon akans akwai yadda ake mu’amala ta ajiyar kudade da kuma musanya gami da saka hannyen jari ta hanyar bankuna, kamar yadda kuma ake nuna musu daga cikin hanyoyi na yadda za a iya yin mu’amala ta banki a zamannance amma bisa koyarwar addini.

3551908


captcha