Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Islamic Movement cewa, waedannan taruka na juyi za su ci gaba har zuwa ranar Ashura, inda za agudanar da babban taro na juyayin shahadar Imam Hussain (AS) da sauran mabiyansa.
Hotunan mabiya tafarkin Shi’a a ranar hudu ga watan Muharram daga garin (Zariya) da ke cikin jahar (Kaduna) a arewacin najeriya.
Birnin Zariya shi ne wuri mafi muhimmanci ga mabiya tafarkin shi’a a Najeriya dake cikin kaduna, Husainiyar (Baqghiyyatollah) shi ne wurin da ake gudanar da babban taron juyayi da sauran tarukan yan shi’a a Najeriya, haka nan kuma a ranar Arba’in a nan ne ake gudanar da babban taro.
Tarukan juyayi da kuma ta’aziyya a birnin (Kano)
Haka nan kuma a sauran birane da kauyuka da yankunan (Katsina) (Potiskum) (Kebbi) da (Shinkafi) da sauransu, na daga cikin inda ake gudanar da taruka na juyayi shahadar Imam Hussain (AS).
3388763