IQNA

Wani harin kunar bakin wake da aka kai a birnin Kabul ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama

17:46 - September 30, 2022
Lambar Labari: 3487935
Tehran (IQNA) Akalla mutane 20 ne suka mutu wasu 35 kuma suka jikkata sakamakon harin kunar bakin wake da aka kai a wata cibiyar ilimi da ke yammacin Kabul, babban birnin kasar Afganistan.

A rahoton Rasha Today, majiyoyin tsaro sun sanar da cewa fashewar ta afku a cibiyar ilimi ta Kaj da ke yammacin birnin Kabul.

Kafofin yada labarai sun sanar da cewa wani dan kunar bakin wake ne ya tayar da bam din.

Kamfanin dillancin labaran Tolo na kasar Afganistan ya kuma bayar da rahoton cewa, dalibai da dama ne suka samu raunuka bayan wani harin kunar bakin wake da aka kai musu a lokacin jarrabawar karatu a wata makaranta da ke yammacin babban birnin kasar.

Wata majiyar gwamnati ta jaddada cewa bayan fashewar bam din, mutane 20 ne suka mutu sannan wasu fiye da 35 suka jikkata.

Khalid Zadran, kakakin 'yan sandan Kabul, ya kuma ce 'yan sanda za su bayar da karin bayani game da fashewar.

Bidiyon da aka buga ta yanar gizo da kuma hotuna da kafafen yada labarai na kasar suka wallafa sun nuna wadanda abin ya shafa sun gudu daga wurin.

Abdul Nafi Takur, kakakin ma'aikatar harkokin cikin gidan Afghanistan, ya wallafa a shafinsa na twitter tun da farko cewa: Tawagar jami'an tsaro sun isa wurin, kuma za a bayyana yadda harin ya faru da kuma cikakkun bayanan wadanda suka mutu.

Kawo yanzu dai babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai wannan harin, amma shekara guda da ta gabata kungiyar ISIS ta dauki alhakin harin kunar bakin wake da aka kai a wata cibiyar ilimi da ke yankin, inda aka kashe mutane 24 ciki har da dalibai.

 

4088746

 

 

 

 

 

 

captcha