IQNA

Sheikh Na'im Qasem: kafa Gwamnatin Hadin Kan Kasa A Lebanon shi Ne Mafita

19:18 - May 23, 2022
Lambar Labari: 3487331
Tehran (IQNA) Mataimakin babban sakataren kungiyar Hizbullah Sheikh Naim Qassem, ya bayyana goyon bayan kungiyar Hizbullah ga shugaban majalisar Nabih Berri domin sake zabensa a matsayin shugaban majalisar wakilai ta kasar, yana mai kira ga sauran bangarorin siyasa da su goyi bayan hakan.

A wata hira da aka yi da shi ta gidan talabijin, Sheikh Qassem ya jaddada cewa, kungiyar Hizbullah tana da zabin da zai kai ga ci gaban  kasar, hakan kuma zai iya tabbata ne ta hanyar aiwatar da abin da yake maslaha ga kasa da kuma makomarta, inda ya ce a bisa wannan manufa muna karfafa kafa gwamnatin hadin kan kasa, kuma abu ne mai wahala kasar ta ci gaba ba tare da gwamnatin hadin kan kasa ba.

Ya ci gaba da cewa, kasar Lebanon ta jima tana fuskantar matsaloli da ake haifar mata daga wajen kasar, da nufin raunana kasar, ta yadda ba za ta iya tsayawa kan kafafunta ba, sai ta dogara ga wasu, wadanda za su rika yi mata shifta da juya akalarta inda suka ga dama.

Y ace yin aikin hadin gwiwa tsakanin dukkanin bangarorin siyasa da al’ummar kasar, shi ne zai iya bayar da damar tunkarar irin wannan kalubale.

Haka nan kuma ya jaddada cewa, dole ne dukkanin bangarorin siyasar kasar su zama wakiltar al’umma, ba masu wakiltar Amurka da Isra’ila ko kuma wasu daga cikin kasashe ‘yan koren Amurka da Isra’ila da suke cikin yankin gabas ta tsakiya ba.

 

4058978

 

captcha