IQNA

Hamas Ta Ce Tana Da Kyakkyawar Alaka Da Iran Da Kuma Hizbullah

23:06 - June 24, 2021
Lambar Labari: 3486046
Tehran (IQNA) Shugaban kungiyar Hamas ya ce suna da kyakkyawar alaka da kasar Iran da kuma kungiyar Hizbullah

Shugaban kungiyar gwagwarmayar Falastinawa ta Hamas Isma’il Haniyya ya bayyana cewa, kungiyar tana da kyakkyawar alaka da kasar Iran, da kuma kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon.

Isma’il Haniyya ya bayyana hakan ne a jiya a birnin Nouakchott fadar mulkin kasar Mauritania, a wata ziyara da tawagar Hamas ta kai a kasar, inda ya jaddada cewa akwai kyakkyawar alaka tun da jimawa tsakanin Hamas da kuma Iran gami da kungiyar Hizbullah.

Ya ci gaba da cewa, Iran tana bai wa Hamas taimako a dukkanin bangarori, da hakan ya hada da makamai da kuma kudade ba tare da Iran din ta gabatar wa Hamas da wani sharadi ko wata bukata ba.

Tawagar Hamas ta kammala gudanar da ziyara a kasar Mauritania a daren jiya, bayan ganawa da manyan jami’an gwamnatin kasar, gami da kungiyoyi da kumawasu daga cikin jam’iyyun siyasar kasar.

Tawagar Hamas za ta gudanar da irin wannan ziyara a kasar Morocco, inda a cikin ‘yan kwanaki masu kuma za ta ziyarci kasashen Iran da Turkiya da kuma Lebanon.

 

3979761

 

 

captcha