IQNA

Za A Yi Wa Jagoran Juyin Musulunci Na Iran Rigakafin Corona Wanda Iran Din Ta Samar

22:55 - June 24, 2021
Lambar Labari: 3486045
Tehran (IQNA) za a yi wa jagoran juyin musulunci na kasar Iran rigafin corona wanda Iran ta samar

Shafin yanar gizo na Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran, ya ce za’ayi wa Ayatullah Sayyid Ali Khamenei, allura ta farko ta rigakafin cutar korona wacce aka samar a kasar samfurin (CovIran Barekat) a cikin kwanaki masu zuwa.

Shafin khamenei.ir ya nakalto Dakta Alireza Marandi, shugaban kwalejin koyon aikin likita na Jamhuriyar Musulunci ta Iran, yana bayyana hakan a jiya Laraba.

“Wannan allurar rigakafin sakamako ne na kokarin matasa masana kimiyyar Iran’’ in ji Marandi.

Dr. Marandi ya ce tun da jimawa ya kamata a yi wa Jagoran allurar rigakafin toh sai dai Jagoran ya ce shi yana so ne a yi masa allurar rigakafin da aka samar a cikin gidan Iran din ba wanda aka shigo da ita daga waje ba.

Ya kara da cewa samar da rigakafin ya sanya Iran ta zama kasa ta shida a duk fadin duniya da ta samu wannan nasarar bayan Indiya, China, Birtaniya, Amurka, da Rasha.

Ma'aikatar Lafiya ta kasar ta amince da allurar rigakafin ta Iran a cikin gaggawa a farkon wannan watan.

 

 

3979758

 

 

 

 

 

 

captcha