Tashar TRT ta bayar da rahoton cewa, a wata ziyara da Ali Arbash shugaban addini na kasar Turkiya ya kai kasar Bulgaria, tare da fitaccen makarancin kur'ani na kasar Usman Shahin, sun gudanar da kiran salla tare a masallacin Muradiyya da ke kasar ta Bulgaria.
Wannan faifan bidiyo ya samu karbuwa matuka tsakanin masu bibiyar shafukan sada zumunta na kasar Turkiya da ma wasu kasashen yankin.