IQNA

Kiran Sallah Tare Tsakanin Shugaban Addini Na Turkiya Da Fitaccen Makarancin Kur'ani

23:43 - June 23, 2021
Lambar Labari: 3486042
Tehran (IQNA) shugaban addini na kasar Turkiya tare da fitaccen makarancin kur'ani na kasar sun gudanar da kiran salla tare a masallacin Muradiyya da ke kasar Bulgaria.

Tashar TRT  ta bayar da rahoton cewa, a wata ziyara da Ali Arbash shugaban addini na kasar Turkiya ya kai kasar Bulgaria, tare da fitaccen makarancin kur'ani na kasar Usman Shahin, sun gudanar da kiran salla tare a masallacin Muradiyya da ke kasar ta Bulgaria.

Wannan faifan bidiyo ya samu karbuwa matuka tsakanin masu bibiyar shafukan sada zumunta na kasar Turkiya da ma wasu kasashen yankin.

3979576

 

captcha