IQNA

Kira Da A Gudanar Da Bincike Kan Mutuwar Alaa Al-Siddiq Mai Fafutukar Kare Hakkin 'Yan Adam A Landan

23:35 - June 22, 2021
Lambar Labari: 3486038
Tehran (IQNA) Masu fafutuka daga sassa daban-daban na duniya suna kiran hukumomin Burtaniya da su gudanar da bincike kan mutuwar fitacciyar mai fafutukar kare hakkin bil adama Alaa Al-Siddiq.

Tashar Russia Today ta bayar da rahoton cewa, masu fafutukar kare hakkokin bil adama daga kasashen duniya suna yin kira ga mahukuntan kasar Burtaniya, kan su gaggauta gudanar da bincike kan mutuwar Alaa Al-siddiq, fitacciyar mai kare hakkokin bil adama a kasar UAE, wadda take zaune a birnin Landan.

Kungiyoyin kare hakkin bil adama da na farar hula daga kasashe daban-daban suna bayyana alhininsu dangane da mutuwar Alaa, sakamkon wani hatsarin mota a kusa da birnin Landan wanda ya yi sanadiyyar mutuwarta a ranar Asabar da ta gabata

Da dama daga cikin kungiyoyin kare hakkin bil adama da ma wasu masu yin sharhi, suna nuna shakku matuka kan yadda hatsarin ya faru, domin kuwa a kowane lokaci Alaa tana bayyana cewa rayuwarta tana cikin hadari, sakamakon yadda jami’an leken asirin UAE da na Saudiyya suke bibiyarta a duk inda take.

Alaa Al-sddiq tana nuna tsananin adawarta da yadda ake take hakkokin jama’a a kasashen larabawa musamman a kasarta ta haihuwa UAE, wanda hakan ne yasa ta bar kasar ta koma kasar Burtaniya da zama, amma duk da haka ana yin barazana ga rayuwarta, wanda yasa wasu suke danganta hakan da irin kisan da hukumomin tsaron kasar Saudiyya suka yi wa Jamal Khashoggi a Turkiya.

Babban abin ya kara bakanta ran mahukuntan UAE dangane da Alaa Al-siddiq a baya-bayan nan dai shi ne yadda take sukar kulla alaka tsakanin Isra’ila da UAE, inda take bayyana hakan a matsayin cin amanar Falastinawa da ma al’ummar musulmi.

 

3979233

 

captcha