IQNA

Ba A Samun Ci Gaba Cikin Sauri A Mu'amalar Kudade Bisa Tsarin Musulunci A Nahiyar Afirka

22:40 - May 25, 2021
Lambar Labari: 3485948
Tehran (IQNA) wata kididdiga ta yi nuni da cewa ba a samun ci gaba cikin sauri a nahiyar Afirka a bangaren hada-hadar kudade bisa tsarin muslunci.

A rahoton da kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar, wata kididdiga da cibiyoyin kula da mu'amalar kudade a bankunan musulunci suka fitar,  ta yi nuni da cewa ba a samun ci gaba cikin sauri a nahiyar Afirka a bangaren hada-hadar kudade bisa tsarin muslunci wanda yake tafiya karkashin bankunan musulunci.

Bayanin ya ce mafi yawan kasashen da suka fi bayar da muhimmanci ga wannan tsari a nahiyar Afirka su ne kasashen arewacin nahiyar, wadanda kasashen larabawa ne musulmi.

Amma kuma bisa la'akari da cewa, akwai kasashe masu yawan musulmi wadanda sun fi na larabawan arewacin Afirka, kamar Najeriya wadda ta fi kowace kasa yawan musulmi a nahiyar Afirka baki daya, amma kason da take da shi a cikin wannan tsarin bai kai yawan da ya kamata ba.

Bayanin ya ce, akwai kasashe wadanda kusan daukacin al'ummominsu musulmi, kamar irin Mali da Senegal da Chadi da makamantansu, wadanda su ma suna a baya a cikin tsarin.

Kasashen yankin gabas ta tsakiya da kuma wasu daga cikin kasashen gabashin Asia irin Malaysia da Indonesia ne dai suka fi kaso mafi tsoka a cikin hada-hadar kudade bisa tsarin muslunci, wanda ake gudanarwa a karkashin bankunan musulunci da kasuwancin kayayyakin halal a kasashen duniya.

 

 

3973229

 

 

captcha