Sakon na jagoran juyin juya hali na kasar Iran ya zo a cikin babban shafinsa na yanar gizo KHAMENEI.IR kamar haka:
Muna taya dukkanin al’ummar kasar Lebanon alhinin abin da ya faru na fashewar wasu abubuwa masu karfi a birnin Beirut, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da jikkatar wasu, muna tare da al’ummar Lebanon, masu hakuri da juriya, kuma muna fatan Allah yasa kare su kuma ya musanya musu asarorinsu da mafi alhairi.