IQNA

Hamas Da Fatah Sun Hada Kai Domin Tunkarar shirin Isra'ila

22:41 - July 02, 2020
Lambar Labari: 3484943
Tehran (IQNA) kungiyoyin Falasdinawa na Hamas da kuma Fatah, sun sha alwashin hada kansu domin tunkarar shirin Isra’ila na mamaye yankunan Falastinawa.

Manyan kungiyoyin Falasdinawa na Hamas da kuma Fatah, sun sha alwashin hada kansu domin tunkarar shirin Isra’ila na mamaye yankunan Falasdinun na yamma da kogin Jordan.

Kungiyoyin wadanda suka shafe kusan shekaru goma basa jituwa tsakaninsu saboda rikicin cikin gisa, sun sanar da hakan ne yayin wani taron manema labarai.

Hakan dai a cewar kungiyoyin wani sabon babi ne na hadin kai a tsakaninsu domin tunkarar haramtaccen shirin yahudawan mamayar na Isra’ila, akmar yadda Jibril Rajub, sakatare janar na kungiyar Fatah ya sanar.

Shi da yake karin bayyani ta kafar bidiyo tun daga birnin Beyrout kan matsayin da suka cimma, Saleh al-Arouri, wani jigo a kungiyar Hamas, ya ce burinsu yanzu shi ne hadin kai da kuma yin magana da baki guda kan batutuwan da suka shafi al’ummar Falasdinu, musamman a wannan lokaci mai mahimmanci.

Marabin dai a yi wata ganawa tsakanin Hamas da Fatah, tun a watan Janairun na 2020.

Shirin Isra’ila na mamayar yankunan Falasdinawa na yamma da kogin Jordan dake cikin yarjejeniyar da shugaba Trump ke kira ta karni, na ci gaba da shan suka daga bangarori daban daban na duniya.

 

3908204

 

Abubuwan Da Ya Shafa: yarjejeniyar Hamas da Fatah falastinawa
captcha