IQNA

Hashd Sha’abi: Fitar Sojojin Amurka Daga Iraki Magana Ce Ta Lokaci kawai

22:48 - June 29, 2020
Lambar Labari: 3484936
Tehran (IQNA) Daya daga cikin manyan  kwamandojin dakarun sa kai na al’ummar Iraki Hashd SHa’abi ya jaddada cewa, ko badade ko bajima sai Amurka ta fice daga Iraki.

Shafin yada labarai na Al-ma’alumah ya bayar da rahoton cewa,a  cikin wani bayaninsa da ya fitar a yau, Ali Hussaini, daya daga cikin manyan  kwamandojin dakarun sa kai na al’ummar Iraki, ya bayyana cewa batun ficewar sojojin Amurka baki daya daga Iraki magana ce ta lokaci kawai.

Ya ci gaba da cewa; kasashen yammacin turai da suka hada da Amurka da kuma wasu daga cikin kasashen larabawa, suna daukar fansa ne a kan dakarun sa kai na al’ummar Iraki, sakamakon yadda suka fatattaki ‘yan ta’addan Daesh daga kasar.

Dangane da hare-haren da aka kai kan sansanin dakarun sa kai Hashd Sha’abi a daren Juma’ar da ta gabata kuwa, ya bayyana cewa wannan duk yana daga cikin makircin da ake kullawa kasar Iraki da nufin tarwatsa ta, da kuma sake bayar da dama ga ‘yan ta’addan Daesh su sake mamaye kasar.

Tun kisan mataimakin babban kwamandan dakarun Hashd Sha’abi Abu Mahdi Muhandis tare da Qasim Sulaimani, majalisar dokokin Iraki ta bukaci Amurka da ta fitar da sojojinta daga Iraki, amma har yanzu tana ta jan kafa kan batun.

 

3907471

 

 

 

 

captcha