Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayar da rahoton cewa, Ilhan Umar yar majalisar dokokin Amurka ta sanar da rasuwar mahaifinta a shafinta na twitter kamar haka:
Ga Allah mu ke kuma lallai mu gare shi za mu koma
Ina bakin cikin sanar da rasuwar mahaifina wanda ya rasu a daren jiya Litinin bayan da ya kamu da cutar corona.
Ihan Umar sun zo Amurka ne tare da mahaifinta a cikin shekara ta 1995, bayan da suka yi gudun hijira daga kasar Somalia zuwa Amurka, inda suka zauna a garin Minneapolis.
Ihan Umar da Rashida Tlaib musulmi ne da suka tsaya takarar majalisar wakilan Amurka a shekara ta 2018, kuam suka samu nasara.