IQNA

Babban Sakataren UN Ya Yi Allawadai Da Hari Kan Masallaci A Burkina Faso

23:28 - October 13, 2019
Lambar Labari: 3484150
Bangaren kasa da kasa, Antonio Guterres babban sakaraeen UN ya yi tir da harin da aka kai kan  masallaci a Burkina Faso.

Kamfanin dillancin labaran iqna, mai magana da yawun babban sakataren UN Sephan Dujareck ya bayyana cewa, Antonio Guterres babban sakaraeen UN ya yi tir da harin da aka kai kan  masallaci a Burkina Faso tare da kashe mutane 16, da kuma jikkata wasu da dama.

Babban sakataren na majlaisar dinkin duniya ya bayyana wanann hari na ta’addanci da cewa babban abin takaici ne, musamamn ganin cewa an kai harin ne kan musulmia  lokacin da suke cikin ibada a masallaci.

Akalla mutane 16 suka rasa rayukansu sannan wasu biyu na daban suka jikkata a wani farmaki da mayaka masu ikirarin jihadi suka kai kan wani Masallaci a arewacin kasar Burkina Faso.

Hukumomin tsaro a kasar sun ce, maharan sun afkawa masu ibadar ne a babban masallacin garin Salmossi da misalin karfe bakawai na daren Juma’ar da ta gabata , inda suka bude musu wuta.

Duk da cewa kasar Burkina Faso na daga cikin kasashen Afrika masu fama da hare-haren ta’addanci, mafi akasarin ‘yan kasar na adawa da kasancewar sojojin kasashen ketare a kasar, musamman na Faransa da ta yi musu mulkin mallaka.

A ranar asabar da ta gabata, kimanin mutane dubu daya suka yi zanga-zanga a Ouagadougou, babban birnin kasar, don yin tir da ta’addanci da kuma kafa sansanonin sojojin kasashen Turai da Amurka a nahiyar Afrika.

3849520

 

 

captcha