IQNA

Mutane Fiye Da Dubu 66 Ne Suka Tsere Daga Birnin Tripoli

23:52 - May 15, 2019
Lambar Labari: 3483642
Bangaren kasa da kasa, mutane fiye da dubu 66 sun tsere daga cikin birnin Tripoli na kasar Libya sanadiyyar hare-haren Haftar.

Kamfanin dillancin labaran iqna, shafin yada labarai na Aljaza'riyya ya bayar da rahoton cewa, daga lokacin da Halifa Haftar ya fara kaddamar da hare-hare kan birnin Tripoli fadar mulkin kasar Libya ya zuwa, mutane fiye da dubu 66 sun tsere daga birnin.

Bayanin ya ci gaba da cewa, dubban mutanen da suka tsere daga gidajensu a ickin birin Tripoli, da dama daga cikinsu suna a tsugunne  halin yanzu a makarantu da kuam wasu gine-gine na gwamnati, yayin da kuma wasu suka fice daga cikin birnin domin tsira da rayukansu.

Halifa Haftar dai yana samun cikakken goyon baya ne da dauki daga kasashen Saudiyya da kuma hadaddiyar daular larabawa, wadanda suke ba shi makudan kudade da kuma tarin makamai.

3811985

 

captcha