IQNA

Hana 'Yar Majalisar Amurka Musulma Zuwa Palastine

19:39 - January 18, 2019
Lambar Labari: 3483324
Wasu yan majalisar dokokin na kokarin ganin an hana Tashida Tulaib 'yar majalisar dokokin Amurka musulma yin tafiya zuwa Palastine.

Kamfanin dillancin labaran iqna, Shafin yada labarai na Dalas News ya bayar da rahoton cewa, Brain Babis dan majalisar dokokin Amurka daga jahar Texas, ya gabatar da bukata ga shugabar majlaisar wakilan Amurka, wadda ta kunshi cewa, suna yin kira da majalisar ta dauki matakin hana 'yar majalisa Rashida Tulaib yin tafiya zuwa Palastine, domin hakan zai iya kawo matsala da rashin jituwa tsakaninsu da babbar kawarsu Isra'ila.

Ya ce bai kamata wani jami'in Amurka ya tafi Palastine domin goyon bayan masu kiyayya da Isra'ila ba, domin hakan yana tattare da hadari ga makomar alaar Amurka da Isra'ila.

Tuna  cikin watan Disamban da ya gabata ne dai Rashida Tulaib wadda 'yar majalisar dokokin Amurka ce musulma kuma 'yar asalin Palastine, ta bayyana cewa za ta tafi Palastine tare da wata tawaga ta masu rajion kare hakkokin bil adama, a daidai lokacin da wata tawagar wasu 'yan majalisar dokokin za su tafi Isra'ila domin kara jaddada goyon bayansu ga Isra'ila.

 

3782206

captcha