IQNA

Japan Ta Bayar da Taimakon Dala Miliyan 5 Ga Musulmin Rohigya

22:55 - January 09, 2019
Lambar Labari: 3483302
Gwamnatin kasar Japan ta bayar da taimakon kudi har dala miliyan 5 ga musulmin Rohingya 'yan kasar Myanmar da suke gudun hijira a Bangaladesh.

Kamfanin dilalncin labaran iqna, Ma'aikatar harkokin wajen kasar Japan ta sanar da cewa, bisa la'akari da cewa kusan fiye da rabin 'yan gudun hijira 'yan kabilar Rohingya da suke a kasar Bangaladesh sun fama da matsaloli musaman na rashin samun abinci mai gin agina, wannan yasa an ware wadannan kudade dala miliyan biyar domin taimaka musu.

Bayanin ya ce gwamnatin Japan ta mika kudaden ne ga hukumar kula da 'yan gudun hijira ta majalisar domin gudanar da wannan aiki, inda hukumar za ta tantance abubuwan da ya kamata a samar musu na abinci ta hanyar yin amfani da wadannan kudade.

Jakadan kasar Japan a kasar Bangaladesh ya ce, mafi yawan abincin da za a samar wa 'yan gudun hijirar manoman kasar Bangaladesh ne za su samar da shi, wanda hakan zai taimaka musu a daya bangaren.

Shi ma  anasa bangaren ministan harkokin wajen kasar Japan Taro Kono ya bayyana cewa, kasarsa tana yin iyakacin kokarinta domin ganin an kawo karshen matsalar da musulmin Rohingya suke ciki, kuma yanzu haka Japan tana tattaunawa gwamnatin Myanmar kan wannan batu.

3779794

 

captcha