Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labaran na Akhbar Iraq ya habarta cewa, ma’aikatar harkokin sadarwa ta kasar Iraki ta sanar a yau cewa ta yi tanadin hanyoyi na yanar gizo kyauta ga masu ziyarar arbaeen a wannan shekara.
Bayanin ya ce a wannan shekara masu ziyara ba za su fuskanci wata masala ta fuskar sadarwa ba, da hakan ya hada da bangaren yanar gizo da kuma layukan wayar salula.
Ma’aikatar sadarwar ta kasar Iraki ta ce za ta saki hanyoyin yanar gizo domin yin amfani da su kyauta a lokacin tarukan arbaeen, domin baki masu gudanar da wannan ziyara su amfana.