IQNA

Babu Barazanar Tsaro A Tarukan Arbaeen A Bana

23:48 - October 18, 2018
Lambar Labari: 3483053
Bangaren kasa da kasa, Mahukuntan kasar Iraki sun sanar da cewa an kammala daukar dukkanin matakan da suka kamata ta fuskar tsaro domin tarukan Arbaeen da za a gudanar a kasar..

 

Kamfanin dillancin labaran iqna, ya bayar da rahoton cewa, manyan jami'an tsaron cikin gida na kasar Iraki sun gudanar da zama, domin tattauna yanayin matakan tsaro a  tarukan Arbaeen da za a gudanar a kasar.

Rahoton ya ce taron wanda ya gudana a karkashin ma'aikatar harkokin cikin gida ta kasar Iraki, ya gamsu da irin matakan da aka dauka ya zuwa yanzu, domin makonni kafin lokacin fara tarukan na Arbaeen, dubban jami'an tsaro suka fara gudanar da ayyukansu a ciki da wajen birnin Karbala.

Taron Arbaeen na cikar kwanaki arba’in da shahadar Imam Hussain (AS) a halin yanzu dai shi ne taro mafi girma da ake gudanarwa a duniya, wanda ya kan hada mutane fiye da miliyan ashirin a lokaci guda a birnin Karbala.

 

3756604

 

 

 

captcha