IQNA

Isra’ila Na Ci Gaba Da Kashe Falastinawa

23:21 - October 17, 2018
Lambar Labari: 3483051
Bangaren kasa da kasa, A ci gaba da kaddamar da hare-haren wuce gona da iri da Isra'ila ke yi kan al'ummar Palastine,a yau wani bafalastine guda ya yi shahada a Gaza.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna, kamfanin dillancin labaran Palastine ya bayar da rahoton cewa, Isra'ila ta kai harin ne da jirgi marassa matuki a cikin Gaza, inda ta kashe wani bafalastine mai suna Muhammad Za'anin mai shekaru 25 a cikin zirin gaza.

Wannan mataki na Isra'ila na ziwa ne a daidai lokacin da take ta kara tsananta hare-harenta kan al'ummar Palastine yankunan zirin Gaza da kuma gabar yama da kogin Jordan.

Koa  ranar Juma'a da ta gabata Isra'ila ta kashe Falastinawa 7 a yankin Zirin Gaza a gangamin da ake gunarwa na neman hakkokin Falastinawa da aka kora daga yankuannsu aka tilasta musu yin gudun hijira, domin su samu dawuwa kaarsu ta haihuwa.

 

3756654

 

 

 

captcha