IQNA

An Rufe Wata Makarantar 'yan salafiyya A garin Durna na Libya

23:53 - August 12, 2018
Lambar Labari: 3482887
Bangaren kasa da kasa, jami'an sojin kasar Libya masu iyayya ga Khalifa Haftar sun rufe wata makarantar 'yan salafiyya a garin Durna.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya haarta cewa, jami'an sojin kasar Libya masu iyayya ga Khalifa Haftar sun rufe wata makarantar 'yan salafiyya a garin Durna sakamakon zargin da ake yin amfani da makarantar domin ayyukan ta'addanci.

Jami'an sojin dai sun dauki wannan matakin ne bayan samun bayanai kan cewa, ana ganin mutane daan-daan wadanda ba 'yan kasar ta Liya ne ba, wadanda suke da kamanni na 'yan ta'adda suna zuwa makarantar.

Wannan makaranta dai an bude ta ne ayan kifar da gwamnatin kasar Libya da 'yan bindiga masu samun goyon bayan kasashen turai da kuma wasu sarakunan laraawa suka yi.

Masu da'awar jihadi da suke tafiya zuwa wasu kasashen yanking abas ta tskiya domin kai hare-hare, sun mayar da wannan makaranta wani zango na su, kamar dai yadda bayanan rundunar sojin suka sanar.

3737631

 

captcha