IQNA

Littafin Wani Farfesa Dan Jamus:

Shin A Cikin Kur’ani Allah Ya Yi Magana Da Kiristoci?

22:32 - February 22, 2018
Lambar Labari: 3482420
Bangaren kasa da kasa, Prof. Klaus von Stosch wani farfesa masani kan addinai a jami’ar Paderborn University da ke kasar Jamus ya rubuta littafi da ke magana kan yadda kur’ani yake kallon kiristoci.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Prof. Klaus von Stosch ya samu babbar kyauta ta Jamhuriyar musulunci ta Iran ta shekara ta 2018, wadda shugaba Rauhani da kansa ya mika masa.

Shugaban kasar ta Iran ya bayyana wannan littafi da cewa shi ne littafin da ya fi dacewa da kyauta a wannan shekara, domin kuwa ya bayyana matsayin kur’ani mai tsarki kan yadda yake kallon sauran addinai da aka saukar daga sama, musamman ma addinin kiristanci, inda ya tabbatar da cewa musulmi da kiristoci ba makiyan juna ba ne.

Haka nan kuma littafin yana kara karfafa zaman lafiya da fahimtar juna a tsakanin bangarorin biyu, ta hanyar tabbatar da hakan daga abin da kur’ani mai tsarki ya fada.

3693579

 

 

captcha