IQNA

Wasu Makaranta Kur'ani 'Yan Afirka Sun Yi Karatu A Mahaifar Abdulbasit

22:22 - February 19, 2018
Lambar Labari: 3482411
Bangaren kasa da kasa, wasu makaranta kur'ani mai tsarki su biyu daga birnin Cape Town na kasar Afirka ta kudu sun ziyarci mahaifar sheikh Abdulbasit Abdulsamad a Masar.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na Almisriyun ya habarta cewa, wadannan makaranta biyu sheikh Ismail da kuma sheikh Munir, a makon da ya gabata ne suka isa kasar Masar inda suka ziyarci mahaifar Sheikh Abdulbasit da ke kauyen Zuraiqat a cikin lardin Alaqsar.

Sun halarci wani taron karatun kur'ani mai tsarki da aka shirya a kauyen, inda suka karanta kur'ani mai tsarki tare da halartar daruruwan mutanen kauyen.

Bayan kammala zaman karatun sun bukaci ziyartar gidan sheikh Abdlbasit, inda suka isa gidan tare da rakiyar jama'a.

Wannan dais hi ne karon farko da wadannan makaranta suke ziyartar kasar Masar, domin kara samun masaniya kan makaranta da suka shahara a duniya musamman Abdulbasit.

An haifi sheikh Abdulbasit a wannan kauye ne tun a cikin shekara ta 1927, kuma ya tashi a matsayin mai son karatun kur'ani, wanda kuma da shi ya shahara a duniya.

3693032

 

 

 

captcha