IQNA

Jagoran Juyin Muslunci:

Sadaukarwar Ali Ridha Karimi Abin Alfahari Ne

21:30 - December 10, 2017
Lambar Labari: 3482185
Bangaren kasa da kasa, jagran juyin juya halin muslunci a Iran ya girmama dan wasan kokowa na kasar Iran Ali Ridha Karimi wanda yaki ya yi wasa da bayahude daga Isra’ila.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin jagora cewa, a yau , jagran juyin juya halin muslunci a Iran Ayatollah sayyid Ali Khameni ya girmama dan wasan kokowa na kasar Ali Ridha Karimi wanda yaki ya yi wasa da bayahuden Isra’ila a wasan kokowar a ‘yan kasa da shekaru 23 ta duniya.

Jagora ya ce hakika abin da wannan matashi ya yi na sadaukarwa da fifita manufa ta koli a kana bin da yake so, wannan ya sanya jin izza da kuma alfahari da ain da wannan matashi ya yi.

Haka nan kuma ya bayyana cewa hakika abin da wannan matashi ya yi saboda Allah ne, kuma Allah madaukakin sarki shi ne mai sakawa da lada, saboda haka yana kira gare wannan matashi da ya tsammaci ladarsa a wajen Allah

Jagora ya ce yana kira ga jami’an gwamnati da kada su yi kasa a gwiwa wajen bayar da kyautuka na musamman ga wannan matashi domin jinjina masa kan namijin kwazon da ya yi., domin kuwa wannan aikin yana matsayin aiki na jarumta ta hakika.

3671223

 

captcha