IQNA

Bude Sabon Studio Na Daukar Karatun Kur’ani A Kazemain

23:30 - October 20, 2017
Lambar Labari: 3482017
Bangaren kasa da kasa, an bude wani sabon studio na daukar karatun kur’ani a karkashin hubbaren Kazemain.
Bude Sabon Studio Na Daukar Karatun Kur’ani A KazemainKamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, ya nakalo daga shafin Qaf cewa, an bude wani sabon studio na daukar karatun kur’ani a karkashin hubbaren Kazemain da ke kasar Iraki, domin daukar shirye-shirye da suka shafi kur’ani mai tsarki.

Bayanin ya ci gaba da cewa, wannan dakin daukar shirye-shirye ya kunshi muhimman kayan aiki na zamani na daukar sauti mai inganci, ta yadda za a iya yin amfai da shi ta hanyoyi da dama.

Daga cikin hanyoyin da za a yi amfani da sautin da za a rika dauka a wannan wuri har da gidajen radio da kuma shafukan yada zumunta gami da shafuka na yanar gizo da suka danganci lamurran kur’ani mai tsarki.

Babbar manufar bude wannan studio da ita ce, kara inganta hanyoyin sauti na karatun kur’ani da ake dauka kuma ake watsa a kafofin yada labara kamar gidajen radio da talabijin da kuma shafukan sadarwa na zamani, ta yadda jama’a za su amfana da wannan aiki.

3654413



راه‌اندازی استودیو اختصاصی دارالقرآن‌الکریم آستان کاظمین


راه‌اندازی استودیو اختصاصی دارالقرآن‌الکریم آستان کاظمین


راه‌اندازی استودیو اختصاصی دارالقرآن‌الکریم آستان کاظمین

captcha