IQNA

Shafukan Google Da Facebook Sun Taimaka Wajen Kara Yada Kyamar Musulmi

23:39 - October 19, 2017
2
Lambar Labari: 3482016
Bangaren kasa da kasa, wasu bayanai daga cibiyoyi daban-daban a kasar Amurka sun tabbatar da cewa shafukan yanar gizo na google da facebook syn taimaka wajen kara yada kyamar msuulmi a kasar Amurka da turai.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na kamfanin dillancin labaran Blooberg ya bayar da rahoton cewa, tun daga lokacin da Trump ya kaddamar da yakin neman zabe, shafukan google da facebook suka fara yi masa kamfe.

Daga lokacin sun rika yada manufofinsa na kin msulunci da tunzura sauran mutane a kan kyamar musulmi, ta yadda hakan ya hada kirkirar hanyoyi na musamman wajen siffanta musulmi da ta’addanci kamar yadda Trump yake kallon dukkanin musulmi.

Dukkanin shafukan biyo sun karfi miliyoyin daloli daga hannun Trump domin gudanar da wannan aiki, da hakan ya hada har jingina tuhumar ta’addanci a kan wasu daga cikin ‘yan jam’iyyar Democrat da suke adawa da Trump.

Ko a baya-bayan nan dai shugaban jam’iyyar Labour kasar Birtaniya Jeremy Corbyn ya kakkausar suka dangane da yadda aka yi amfani da wadannan shafukan yanar gizo da suke da karbuwa a duniya domin bata sunan musulmi.

3654564


Wanda Aka Watsa: 2
Ana Cikin Dubawa: 0
Ba A Iya Watsa Shi: 0
dahirou
0
0
dasannu adinin musilinci saiyagama duniya cir d'à halin kafiray
dahirou
0
0
dasannu adinin musilinci saiyagama duniya cir da halin kafiray
captcha